Tsaro
Ya kamata a daina jin tsoron ƴan bindiga- Ministan tsaro
Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su tunkari ƴan bindigar da suka addabe su.
BBC, ta ruwaito cewa, Ministan ya ce ƴan bindigar da suka sace ɗaliban makarantar sakandiren kwana ta Kagara da ke jihar Neja matsorata ne.
Haka kuma ya ƙara da cewa kowane ɗan Najeriya na da alhakin tabbatar da cewa akwai matuƙar tsaro a wurin da yake rayuwa.
Ya kuma ce, haƙƙin kowa ne ya yi taka tsan-tsan domin tabbatar da tsaro ba wai dakarun soji kaɗai ba.
Manjo Magashi mai ritaya ya ƙara da cewa “Bai kamata mu zama matsorata ba, don kuwa wani lokacin ƴan bindigar na kai farmaki ne da harsasai 3 kacal, amma idan suka harba ɗaya sai duk mutane su tsorata.”
Haka kuma ya ce yan bindigar za su fara tsoron mutanen gari da zarar an fara tunkararsu.
