Tsaro
Kano: Rundunar tsaro ta Civil Defence ta Cafke gawurtaccen ɓarawo
Rundunar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta Cafke wani matashi Ibrahim Bala wanda ya ƙware wajen ɓalle kayan aikin ginin gidaje.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana haka ga manema labari yau Talata.
Ya ce, tun da fari sun cafke matashi ne bisa zargi haura rukunin gidaje na Gurjiya da ke yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu yana yin sata a lokuta daban-daban.
Haka kuma ya ce, kayan da ma tashin ke sacewa sun haɗar da Ƙofofi da Tagogi har ma da sauran kayan gine-gine, kuma tuni rundunar ta kama wasu mutane 3 da yake sayar wa kayan.
A nasa ɓangaren, Ibrahim Bala d ya ce, shi ɗan mazaunin ƙauyen Gurjiya ne, ya amsa cewa tabbas shi yake sace kayan har ma ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya sata.
DSP Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce rundunar tsaron ta Civil Defence, z ta gurfanar da waɗand ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
