Labarai
Shugaba Buhari ya dawo Najeriya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan da ya shafe kwanaki 16 da yin balaguro.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, shugaban ƙasar ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 4:45 na yammacin yau Talata.
Tun da fari dai, shugaban ya halarci taron zaman lafiya a birnin Glasgow na ƙasar Scotland.
Haka kuma bayan kammala taron ne ya wuce ƙasar Faransa domin wata ganawa da shugaban ƙasar Mista Emmanuel Macron, sannan ya bi ta ƙasar Afirka ta Kudu inda ya halarci bikin baje koli.
