Labarai
Kano: Hukumar PHIMA ta rufe asibiti mai zaman kansa
Hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano PHIMA, ta kulle wani asibiti mai zaman kansa Al-ziyadah clinic da ke yankin Naibawa ƴan katako a yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.
Mai magana da yawun hukumar Malam Abba Dalha, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba ya wa manema labarai yau Alhamis.
Sanarwar ta ce, hukumar ta rufe asibitin ne sakamakon wasu rahotonnin aikata abubuwan da ba su dace ba a asibitin tare da rashin bai wa marasa lafiya kulawar da ta dace da kuma rahoton tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma sanarwar ta ce, asibitin zai ci gaba da zama a garƙame har zuwa lokacin da aka kammala bincike a kansa.
