Connect with us

Labarai

Borno: Sojoji sun daƙile harin ƴan tada ƙayar baya

Rahotonni daga garin Damboa a Jihar Borno na nuni da cewa mazauna garin sun wayi gari cikin murna bisa nasarar da sojoji suka samu ta daƙile wani harin ƴan tada ƙayar baya da ke iƙirarin jahadi suka yi yunƙurin kai wa garin da safiyar yau Juma’a.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa ƴan tada ƙayar bayan sun afka garin ne da misalin ƙarfe 6:35 na safiya inda suka yi ta harbe-harbe, sai dai sun tsere kimanin minti 30 bayan da dakarun tsaron suka fi ƙarfinsu.

Jaridar ta ruwaito cewa maharan sun afka wa garin da misalin ƙarfe 6:35, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi.

Haka kuma ta ruwaito cewa, a Asabar ɗin da ta gabata ne rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe gwamman mayaƙan ISWAP da suka kai wa sansaninta hari a Askira, sai dai lamarin ya yi sanadiyyar kashe Birgediya Janar Dzarma Zurkushu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet