Ilimi
Gwamnatin Buhari ta baiwa jami’ar FUD da ke Jigawa Naira biliyan 10
Gwamnatin tarayya ta amince da baiwa jamiar tarayya dake Dutse kudi naira miliyan dubu goma domin daga darajar asibitin koyarwa na jamiar.
Mataimakin shugaban jamiar Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad ya sanar da hakan ta cikin shirin radio jigawa na mako mako mai suna Mai Damarar Aiki.
Yace tuni suka karbi wani bangare na kudade inda suka fara gine gine da sayen naurorin aikin kiwon lafiya daban daban.
Farfesa Abdulkarim Sabo ya kara da cewar gwamnatin jihar jigawa ta amince da basu karin fili domin gudanar da gine gine
Yace asusun tallafawa ilmi na kasa yana baiwa jamiar kudade domin gudanar da gine ginen ajujuwa da tura malamai karo ilmi.
A cewarsa jamiar ta kammala shirye shirye bude karin tsangayoyin karatun aikin lawya dana kimiyyar harhada magunguna a shekara mai zuwa
Mataimakin shugaban jamiar yace sun bullo da tsarin koyarwa na zamani ga dalibai domin samun saukin karantar da dalibai.
Yace zasu fara daukar sabbin dalibai na shekarar karatu ta 2021/2022 nan da wasu makonni
Inda kuma ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa tallafin da yake baiwa jamiar a kowane lokaci
