Featured
Mata Da Sana’a: Yadda wata matashiya ta rungumi sana’ar yin Fura da Yoghurt a Kano
A wannan makon filin mata da sana’a na kamfanin WhiteBlood Multimedia Service masu mallakin shafin jaridar Kakaki Hausa ya samu zarafin tattaunawa da wata matashiya mai suna Maria Musa, shugabar kamfanin Eaman Food and Dairy Products, da ke birnin Kano a Arewacin Najeriya.
A cikin tattaunawar tamu da wannan matashiya ta bayyana mana yadda ta tsunduma wannan kasuwancin bayan kammala digirinta na farko a ɓangaren tattalin arziki da harkar noma da ke jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudil, a jihar Kano.
Haka kuma Maria ta ce ita kam yanzu Alhamdulillah domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, la’akari da yadda ta ke kai kayayyakin da ta ke sarrafawa zuwa wasu jihohin baya ga jihar Kano.
Ga dai yadda tattaunawar tamu ta kasance tare da ita:
Kakaki Hausa: Ya sunan matashiyar?
Maria Sani: Sunana Maria Musa mamallakiyar kamfanin Eaman Food and Dairy Products.
Kakaki Hausa: Ko za ki sanar da masu karatu taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
Maria Sani: Kamar yadda na gaya maka da farko sunana Maria Musa mamallakiyar kamfanin Eaman Food and Dairy Products, kuma yanzu haka ina da shekara 22 a duniya. Na yi karatu a jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudil, a jihar Kano. Wato Kano State University of Science and Technology, Wudil (KUST WUDIL. Kuma na samu nasarar kammala karatuna a ɓangaren tattalin arziki da harkokin noma wato Agricultural Economic and Extension, kuma cikin ikon Allah na kammala wannam karatu a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 2021 .
Kakaki Hausa: Wacce sana’ar ce ki ka yi fice?
Maria: Sana’ar da aka fi sani na a kai ita ce sana’ar madara kamar su Kindirmo da Yoghurt da Fura da Man Shanu da kuma danyar Madara. A ɗaya ɓangaren kuma ina taɓa sana’ar sayar da turarurruka.
Kakaki Hausa: Wacce nasara ki ka samu a wannan sana’a?
Maria: Alhamdulillah na samu nasara cikin sana’ar nan saboda lokacin da na fara a gida kadai na ke saidawa, daga nan kuma na fara kai kaya na wani babban shago. Yanzu kam Alhamdulillah kayana suna fita har zuwa wasu jihohin da sauran garuruwa.

Kakaki Hausa: Waɗanne ƙalubale ki ke fuskanta a harkokin wannan sana’a?
Maria: Babu shakka kowacce sana’a ba za ka rasa ta da ƙalubale irin na ta ba, wanda ya haɗa da mu’amala da mutane da yadda za ka aike da kayanka zuwa wani gari da kuma sauran matsaloli nan da can. Amma Alhamdulillah muna bakin kokari wajen kau da dukkanin matsala da za ta kawo cikas a wannan kasuwanci na mu.

Kakaki Hausa: Menene babban burinki a kasuwanci?
Maria: Baban burina a rayuwar kasuwancina shi ne na zamo ina taimakawa kaina da iyayena da ma sauran al’umma wannan shi ne dalilin da ya sa na fara sana’a.
Kakaki Hausa: Menene abin da ki ka fi so?
Maria: Ina son gaskiya da rikon amana wanda shi ne jigon lafiya da ƙaruwar cigaban arziki na kowacce irin al’umma.
Kakaki Hausa: Menene abin da ba kya so?
Maria: Abin da ba na so shi ne ƙarya da ha’inci shi ya sa na ke son a gaya min gaskiya komai ɗacinta ko da kuwa ba zan yarda ba.
Kakaki Hausa: Wacce kala ki ka fi so?
Maria: Ina son kalar ruwan ganye saboda yana sanya ni cikin nishaɗi haka kuma ina son Royal Blue!
Kakaki Hausa: Menene Kiranki ga matasa?
Maria: Kirana ga matasa shi ne su tashi su kama sana’a a kowanne irin halin rayuwa suka samun kansu, don ta haka ne kawai za su iya zama wani abu a rayuwa. Kuma babban abin la’akari da shi a nan shine ka da su bar karatu, don idan ka kasance kana sana’a amma kuma babu karatu to ba za ka ji dadin tafi da al’amuran yadda ya kamata ba, saboda karatu na da matukar mahimanci, don a lokuta da dama wasu abubuwan ba za ka iya yin su ba har sai ka na da ilimi.

