Connect with us

Featured

Mu Tashi Mu Farka Ƴan Arewa: Yadda wata sabuwar matsala ta tunkaro arewacin Najeriya

Akwai wata babbar matsala da ta ke kokarin tunkaro mu a Arewa da ya kamata mu tashi tsaye don magance ta.

Jiya na ga wata wallafa a shafin Facebook akan cewa duk ƴan ta’addar da su ka fitini Arewa Fulani ne da Kanuri da sauran ƙabilu amma babu Hausawa. Da na yiwa abin kallon ƙarancin tunani na wasu wawaye daga cikinmu. Amma bayan da na zurfafa bincike sai na gano cewa wata shiryayyiyar makarkashiya ce da ake son yin amfani da ita don a yake mu. Daga jiya zuwa yau na gano Facebook accounts waɗanda aka kirkira don yaɗa gaba da kiyayya musamman tsakanin Hausawa da Fulani.

Abun takaici shi ne yadda wasu da nake yi wa kallon masu hankali naga suna “liking” irin wadannan post din. Wasu ma har karfafawa masu post din gwiwa su ke yi.

To a nan ina so na yi mana wata matashiya. Idan muka duba da kyau za mu ga cewa babban abin da Arewa ta ke alfahari da shi shi ne yawan jama’a da kuma haɗin kai. Ko da yake dai an riga an ci nasarar raba kan mu ta ɓangaren addini yadda yanzu haka babu wata yarda mai karfi tsakanin mafi yawan Musulmi da Kiristocin Arewa. Sannan tsakanin musulman ma bambamcin akida yana kara zafi da raba kawunan mu. Amma duk da haka hatsarin irin waɗannan rabe-raben bai kai na rabuwar kan Hausawa da Fulani da Kanuri da sauran kabilu ba.

Tabbas daga ranar da aka ce Bahaushe ya fara yi wa Bafulatani ko Kanuri kallon abokin gaba to ƙarshen Arewa ya zo. Don haka idan ma siyasa ce ta sa wasu suke so su ɓullo da wannan masifar to su sani cewa bala’in da za su zungoru sai ya shafi har jikokinsu. Idan kuma wasu mutane ne daga wani ɓangare na ƙasar nan su ke son yin amfani da wannan damar don raba kawunanmu to ya kamata waɗanda ake amfani dasu a cikinmu su farga su gane illar yin hakan.

A ƙarshe, ina kira ga musamman matasa da su rinka yin taka-tsantsan akan irin waɗannan lamuran kafin su jefa kawunansu cikin masifar da ba za su iya fita ba. Kuma duk Musulmin da yayi Imani da Allah to ya sani cewa ba don wani abu U’ubangiji ya halicce mu kabilu daban-daban ba sai don kawai mu samu sauki wajen bambamce junanmu. Haka kuma Annabi Muhammad (SAW) ya yi hani da kabilanci. Don haka sai ku nemawa kanku madogara.

Allah Ya sa mu gane kafin mu makara.

Idris Hamza Yana, Malami ne a jami’ar Sule Lamido da ke ƙaramar hukumar Kafin – Hausa a jihar Jigawa

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet