Connect with us

Labarai

Filato: Ƴan bindiga sun hallaka mutane 10 a wani hari

Wasu ƴan bindiga da sanyin safiyar Juma’a sun kashe mutane 10 a kauyen Ta’agbe da ke masarautar Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Uba Ogba, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a birnin Jos.

Ogaba ya ce, kwamishinan ƴan sandan jihar, ya koma inda lamarin ya faru.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ya tura ƙarin jami’ai yankin domin daƙile taɓarɓarewar tsaron da wurin ya gamu da shi.

A martaninsa kan lamarin, Danjuma Auta, babban sakataren kungiyar ci gaban Iregwe IDA, ya bayyana damuwarsa kan faruwar lamarin.

Ya ce, “Ya zama dole al’ummar Irigwe su sake rubuta sanarwa tare da bayyana irin ƙuncin da muke da shi game da sabbin hare-haren da ake kaiwa jama’armu ba tare da wani dalili ba, bayan da suka samu kwanciyar hankali na ƴan makonni”.

“Da safiyar yau ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Ta’agbe kuma a halin yanzu mun tabbatar da mutuwar mutane 11 yayin da ake ci gaba da bincike,” inji shi.

Auta ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an ceto rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet