Tsaro
Gwamnatin Kaduna ta sanar da dawo da ayyukan sadarwa
Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce ta tuntuɓi hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa domin ganin ta gaggauta maido da ayyukan sadarwar da aka dakatar a wasu ƙananan hukumominta.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana dawo da harkokin sadarwar yau Juma’a yayin taron manema labarai.
Ya ce “Matakan da aka ɗauka na tabbatar da tsaro, musamman rufe hanyoyin sadarwa ya taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasarori kuma za su ƙara haifar da kyawawan sakamako ga jami’an tsaro nan ba da jimawa ba.”
“An shawarci mazauna yankin da cewa maido da cikakken ayyuka a yankunan da abin ya shafa na iya bayyana a cikin ƴan kwanaki, yayin da kamfanonin sadarwa ke yin ƙoƙarin ƙara i ga ta ayyukansu dai-dai da yadda ya dace.” inji kwamishinan.
Haka kuma ya ce, Gwamnatin jihar na fatan yaba wa sadaukarwar da mazauna yankin suka yi yayin da wannan matakin na wucin gadi ya dade.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan Oktoban da ya gabata ne hukumomin tsaro suka buƙaci a toshe hanyoyin sadarwar a wasu yankuna domin magance ayyukn ƴan bindiga da sauran laifuka a jihar.
