Connect with us

Labarai

Tsananin ƙiyayyar juna ga wasu ma’aurata ta sanya kotu raba aurensu

Wani mutum mai suna Fasto Adekunbi Osho ɗan kimanin shekaru 45 ya samu biyan bukatar sa bayan da wata kotu da ke zamanta a yankin Igando a jihar Legas ta raba auren sa na shekara shida da matarsa Rebecca.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya warware kullin wannan auren ne bayan dagewar da Fasto Adekunbi Osho ya yi na lallai kotu ta raba aurensa duk da rokon da aka yi ta yi.

A bayanin da ya yi wa kotun Fasto Adekunbi Osho ya ce matarsa Rabecca ta ki jinin ta gan shi yana samun ci gaba a rayuwa da kuma gurin aikinsa.

Ya ce zargin fasikancin da Rabecca ta ke yi masa ya sa ba a yi masa ganin mutumin kirki ballantana a ƙara masa girma a wurin aiki.

“Rabecca ta rubuta wasiƙa ga fastocin cocin da nake aiki da su da shugaban cocin cewa ni kasurgumin manemin matane sannan ta yi min sharri wai na taɓa aika mata da yan iska su kashe.

“Wata rana Rabecca ta taɓa dalla min mari ta kuma yayyaga mun riga a cikin jama’a saboda wai ta kama ni da wata mata.

Fasto Adekunbi Osho ya ce Rabecca masifaffiyar mata ce wacce bata ƙaunar ƴan uwansa domin hatta ƴar su ɗaya da suka haifa ma ba ta so ya kusance ta.

Ya ce ya gaji da auren kuma yana rokon kotu ta bashi damar kula da ‘yar ta su guda daya mai shekara 3 da suka haifa tare.

Rabecca mai shekara 36 ba tace komai ba game da hujojjin da mijinta ya bada a kotun.

Sai dai ta ce ta hana Osho taba ‘yar su ne saboda ba shine mahaifinta ba.

“Wani saurayi na ne ya yi mun ciki a lokacin da nake auren Osho da hakan ya sa bazan bari ya goya dan wani ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet