Labarai
Cutar Korona samfurin Omicron ta ɓulla a Najeriya: Mutum uku sun kamu
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta sanar da karin wasu mutum 105 masu kamuwa da COVID-19 yayin da ta gano uku daga ciki da nau’in Omicron COVID-19 a cikin kasar.
NCDC ta ba da wannan adadi ne a cikin rahotonta na yau da kullun na COVID-19 a ranar Laraba a Abuja.
Cibiyar ta yi gargadin cewa Najeriya na cikin hadarin yin karuwar yawan masu kamuwa da sabon nau’in saboda rashin kula da matakan kariya a tashoshin jiragen sama da sauran wuraren shiga kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa karin masu Cutar 105 da aka bayar a ranar Talata, ya karu daga mutum 21 da aka samu a kasar a ranar da ta gabata.
Sabbin alkaluma sun nuna cewa kasar a yanzu tana da jimillar mutane 214,218 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19.
A cewar hukumar, an sami sabbin cututtukan a cikin jihohi takwas da babban birnin tarayya (FCT).
Ta kara da cewa an samu sabbin kararraki na COVID-19 kamar haka: Legas (43), Gombe (21), FCT (16), Niger (10), Rivers (6), Plateau (5), Edo (2), Bauchi (1), da Kano (1).
NCDC ta ce mutane 12 sun murmure daga kamuwa da cutar ya zuwa ranar Talata, yayin da adadin wadanda aka sallama yanzu ya kai 207,304 a fadin kasar.
Ta kuma kara da cewa an samu mutuwa sakamakon COVID-19 guda daya da aka bayar a ranar Talata wanda ya bar adadin wadanda suka mutu ya kai 2,977.
Hukumar ta kara da cewa an gwada gwajin jinin mutane 3,479,682 tun bayan barkewar cutar a fadin kasar. Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (EOC) mai sassa daban-daban da ke a mataki na 2, za ta ci gaba da daidaita ayyukan yaki da cutar a kasar.
Tun bayan bullar Omicron, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta hanyar NCDC ta tsaurara matakan yaki da COVID-19 a cikin kasar.
Kwamitin Shugaban Kasa (PSC) ya sake sabunta shawarar tafiye-tafiye na kasa da kasa kan COVID-19 kuma a yanzu yana buƙatar duk matafiya masu shigowa Najeriya da su gabatar da sakamakon gwajin COVID-19 da sa’o’i 48 kafin tashin jirgin su.
Hakanan duk fasinjojin da ke fita ba tare da la’akari da buƙatun ƙasashen da za su nufa sai sun gabatar da shaidar cikakken rigakafin ko gwajin COVID-19 PCR da aka yi musu a sa’o’i 48 kafin tashi.
Gwamnati ta yi kira ga ‘yan kasarta da su bi wadannan ka’idojin tafiya da sauran matakan kare lafiyar jama’a. Ya kara da cewa idan aka yi la’akari da haɗarin haɓakar cutar Omicron, yana da mahimmanci a dauki mataki don hana yaɗuwar ta a cikin al’umma.
