Uncategorized
Babu wanda ya kama Abdullahi Abbas – APC Ɓangaren Ganduje
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta jihar Kano, ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Ahmad S Aruwa, ya bukaci al’umma da su yi watsi da wani labari da ake cewa jami’an tsaro sun kama shugabansu na APC, Abdullahi Abbas, inda ya ce labari ne mara tushe balle makama.
Aruwa yace Abdullahi Abbas yana Abuja yanzu haka, suna tare da gwamna Ganduje a wata ziyarar aiki da suka kai, ciki harda batun daukaka kara akan hukuncin kotu na sha’anin zaben shugabannin mazabu na jam’iyyar APC ta jihar Kano.
Kakakin jam’iyyar, ya kara da cewa, ko jiya sunyi dashi, yau ma da safe sunyi waya, kuma zasu yi kokari wajen ganin mutane sun saurari muryarsa, hakazalika yace tuni sun shiga binciken masu yada labarin an kama shugaban nasu, domin daukar matakin doka.
