Labarai
Ƴan sanda sun cafke mai wankin motar da ya gudu da motar Naira Miliyan 8 a Kano
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wani matashi mai wankin mota, Abdullahi Sabo bayan da ya arce da motar wata mata, wacce kuɗin ta ya kai naira miliyan 8 da dubu 500.
Jaridar Daily Nigerian ta rawiato cewa an kama ɓarawon, ɗan shekara 30, a garin Daura dake jihar Katsina tare da motar, wanda dan asalin garin ne.
A sanarwa da Kakakin Rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Laraba, rundunar ta ce a ranar 30 ga watan Nuwamba ne ta samu ƙorafin daga wata mazauniyar unguwar Badawa, cewa wani mai wankin mota ya gudu da motar ta ƙirar Honda Accord 2017 wacce kuɗin ta ya kai miliyan takwas da rabi.
A yayin bincike, in ji Kiyawa, sai rundunar ta yi sammacin mai wajen wankin motar, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki wani Abdullahi aiki alhalin bai san shi ba.
Ya ƙara da cewa a ranar, ya shiga cikin gidan wankin motar ya bar shi a waje yana wanke motar saboda amincewa, amma daga nan sai ya tsere da ita.
Kiyawa ya ce mai laifin ya amsa laifin sa cewa tabbas ya gudu da motar da niyyar ya sayar da ita.
