Labarai
Ƙungiyar Human Rights ta karrama Ƴar Jarida Zainab Abdulrahman Mai Agogo a Kano
Wata ƙungiyar kare hakkin bil adama mai mazauni a birnin Kano, Global Community for Human Rights Network (GCHR), ta karrama shugabar kamfanin WhiteBlood Multimedia Service, Hajiya Zainab Abdurrahman Mai Agogo, bisa jajircewar ta wajen taimakon al’umma tare da ganin an ƙwatowa mai haƙƙi haƙƙinsa.
Shugaban ƙungiyar ta GHCR Karibu Lawan Yahaya Kabara, ya ce sun zaɓi ranar 10 ga watan Disamba wacce ta kasance ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe a matsayin ranar Ƴancin Bil’adama ta Duniya, dan gudanar da wannan gagarumin biki.
Shugaban ya ƙara da cewa wajen karramawar sun zaɓi fitattun mutane da kuma ƴan jarida daga kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya, da su ka yi fice wajen kare hakkin bil’adama tare da taimakawa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma.
A cikin waɗanda ƙungiyar ta karrama akwai babban Editan sashen Hausa na BBC Malam Aliyu Abdullahi Tanko da Bilkisu Babangida da Yusuf Ibrahim Yakasai da kuma Abdullateef Abubakar Jos.
Zainab Abdurrahman Mai Agogo ita ce mamallakiyar kamfanin WhiteBlood Multimedia Media, wanda a ƙarƙashin wannan kamfani akwai Farin Jini TV da Kakaki Hausa.
Haka kuma Zainab Mai Agogo ita ce ke riƙe da matsayin ma’ajin kuɗi na ƙungiyar ƴan jaridu masu gudanar da ayyukansu a shafukan Intanet, reshen jihar Kano. Kuma ƴar jarida ce da ta karɓi zamani da kuma amfani da sauyin da zamanin ya zo da shi a harkokin aikin jarida.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ware ranar 10 ga watan Disambar kowacce shekara domin nazari a kan take hakkin bil adama a duniya.
Ana kallon wannan rana a matsayin wata gagarumar nasara ce wurin tabbatar duk al’ummar duniya suna samu ƴancin su da Allah ya basu ba tare da la’akari da jinsi ko launi ko addini ko harshe ko siyasa ko kuma yanayin da mutum ya tsinci kansa a ciki ba.
