Connect with us

Labarai

Plateau: Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutum Tara, Tare Da jikkata Wasu Da Dama

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Pinau da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, wasu mutane 9 ne suka mutu sannan wasu hudu suka jikkata.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Filato, Gabriel Ubah, ya ce an tura da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa kauyen da ke masarautar Mavo.

Ya bayyana cewa an kama mutane takwas da ake zargi da kai harin, an kuma kwato babura 12 daga hannun maharan.

A cewar Ubah, ana cigaba da gudanar da bincike a yunkurin da ake na cafke wasu da ake zargi da guduwa yayin da kuma aka tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana barkewar rikici.

“A jiya, da misalin karfe 4:30 na rana, sai muka samu kiran waya cewa wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun kai farmaki kauyen Pinau da ke karamar hukumar Wase. Abin takaici, sun kashe mutane tara yayin da mutane hudu suka jikkata,” in ji sanarwar.

“Bayan samun labarin, rundunar ‘yan sandan hadin gwiwa, da jami’an ‘Operation Safe Haven (OPSH),’ da sauran jami’an tsaro da aka tattara tare da garzaya da su wurin. An kama mutane takwas da ake zargi, an kuma kwato babura 12 a wurin.”

A halin da ake ciki mataimakin kakakin majalisar wakilai Ahmed Idris Wase mai wakiltar Wase ya yi Allah wadai da harin. Ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa ya fitar, ya bayyana harin a matsayin rashin mutuntakmwa, rashin hankali, da rashin sanin yakamata, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

A cewar sa, harin na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ta kokarin ganin sun samu abun dogaro da kai.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet