Uncategorized
Babu wani shugaba da zai iya kawar da ƴan bindiga a Najeriya – Fadar Shugaba Ƙasa
Ministan yada labarai na Najeriya Lai Mohammed ya ce babu wani shugaba da zai ce ayyukan ta’addanci za su gushe a shekara mai zuwa.
Ministan yana mayar da martani a kan tambayar da aka mai a wani taron manema labarai cewa ko kalubalen tsaron da ake fuskanta a halin yanzu zai kare kafin shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a kan karagar mulki a shekarar 2023.
Lai ya ce ba ya tsammani ko shugaba Buhari zai iya cewa za a dakile ayyukan ‘yan bindiga a shekara mai zuwa, yana mai cewa tamkar a ce za a kawar da barayi ne a shekara mai zuwa.
Ministan ya ce, cewa Buhari ba shi da sauran wani abin da zai tabuka a kasar ba gaskiya bane, hassada ce irin ta siyasa.
Idan ba a manta ba, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya shaida waw ani taron zaman lafiya cewa Buhari ya yi iya kokarinsa, kuma babu wani abin da zai iya yi a nan gaba.
