Connect with us

Labarai

Hukumomin Ƙasar Koriya Ta Arewa Sun Haramtawa Ƴan Ƙasar Yin Dariya Na Tsawon Kwanaki 11

Rahotannin daga kasar Korea ta Arewa na cewa an dakatar da kafatanin ‘yan kasar daga yin dariya tare da hana su shan barasa na tsawon kwanaki 11 domin zagayowar bikin cika shekaru goma da rasuwar tsohon shugabansu Kim Jong II.

KakakiHausa ta rawaito cewa, wannan umarni na haramtawa ‘yan Koriya ta Arewa nuna farin ciki, hukumomin gwamnatin kasar ne suka bayar da shi domin tunawa da mutuwar Kim Jong II, wanda ya mulki kasar daga shekarar 1994 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2011.

Bayan mutuwarsa, dan sa wanda shine shugaban na yanzu Kim Jong Un, kuma ɗansa na uku sannan shine ƙarami, ya karɓi ragamar shugabancin kasar.

“A lokacin zaman makoki, bai kamata mu sha barasa ba, ko mu yi dariya ko kuma shagaltuwa da sha’awa,” kamar yadda wani dan Koriya ta Arewa daga birnin Sinuiju dake kan iyaka da arewa maso gabashin Asiya ya shaida wa gidan rediyon Free Asia.

Majiyar ta kara da cewa, “A baya, an kama wasu mutane da dama suna shan giya ko kuma suna buguwa a lokacin zaman makoki, ana daukarsu a matsayin masu aikata miyagun laifuka wanda hakan yasa aka tafi dasu bayan haka ba a sake ganin su ba.
“Ko da danginku ya mutu a lokacin zaman makoki, ba za a barku ku yi kuka da babbar murya ba, kuma dole ne a fitar da gawar bayan an gama shirya ta zuwa masaukin ta.

Kazalika “Mutane ba za su iya yin bikin ranar tunawa da haihuwarsu ba idan sun fada cikin lokacin zaman makoki.”

Majiyar ta kuma bayyana cewa an haramtawa ‘yan Koriya ta Arewa zuwa siyayyar kayan abinci a ranar 17 ga watan Disamba – daidai da ranar da tsohon shugaban ya mutu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet