Connect with us

Tsaro

Wani Sifeto Ya Rasa Ransa A Wani Hari Da Aka Kai Ofishin Ƴan Sanda

An kashe wani sifeto da wasu mutane biyu a wani hari da aka kai a ofishin ‘yan sanda a jihar Kogi, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga hare-haren ‘yan fashi da makami a bankuna biyu a Odo-Ere da Egbe.

Aya ya bayyana cewa, an kai harin ne a ranar Talata a karamar hukumar Yagba ta Yamma da ke jihar.

Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda sun fara farautar wadan da ake zargin tare da hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, da mafarauta da ‘yan banga da ke neman ‘yan bindigar da aka ce sun tsere zuwa tsaunuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, an kama biyu daga cikin wadan da ake zargi, an kai su ofishin ‘yan sanda na Odo-Ere, biyo bayan binciken da wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sandan ya yi ta sama tare da jami’an tsaro na musamman.

Sai dai ya ce wasu gungun jama’a ne suka kai farmaki ofishin ‘yan sandan, inda suka bukaci da a ba su mutane biyu da aka kama don su yi musu kisan kiyashi.

Yayin da kokarin ‘yan sandan kwantar da tarzoma ya ci tura, Aya ya ce sun yi tashin hankali inda aka kashe sufeto Bamisaye Gbenga, sannan wani dan sanda Sunday Alechenu ya samu rauni.

A cewar Aya, mutane biyu – namiji da mace – suma sun sami raunuka a kokarin tarwatsa ‘yan ta’addan. Amma daga baya sun mutu a asibiti yayin da ’yan bangar suka cinna wuta a wani bangare na ofishin.

Rundunar ‘yan sandan ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ginin ta tare da yin kira ga mazauna Odo Ere musamman matasa da su guji daukar doka a hannunsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet