Labarai
Gwamnatin Jihar Nassarawa ta haramta sayarwa ko amfani da gawayi
Bayan da yanayin sanyi ya sawo kai a yankin Arewacin Nijeriya, Gwamnatin Jihar Nassarawa ta hana sayarwa da amfani da gawayi a faɗin jihar domin inganta muhalli.
Aliyu Agwai, Babban Sakataren Maikatar kula da Muhalli da Ma’adanai ne ya sanar da hakan a taron ganawa da manema labarai a Lafiya.
Ya ce hanyar da ake bi a ke yi gawayi na cutar da muhalli ta hanyar gurɓata iska da kuma ƙarawa yanayi zafi.
Agwai ya ƙara da cewa ƙona gawayi na haifar da gurɓatacciyar iska mai cutar da ɗan adam.
“Sare bishiyoyi na lalalata muhallin dabbobi wanda hakan ke illata muhalli,” in ji Agwai.
Galibi talakawa wadanda su ne suka fi yawa, na dogara da kalanzir wajen amfanin yau da kullum na girke-girke, wanda kuma ƙarancinsa kan tilasta wa wasu amfani da itatce, ko gawayin kwal da kuma iskar gas
