Connect with us

Featured

Ra’ayi: Duk Musulmar da ta fito takarar ‘Sarauniyar Kyau’ mummunar munafuka ce

A tarihi irin na Addinin Islama, ba bu wani zamani da aka taba yi wanda mata ‘musulmi’ suke fitowa, ko shiga wata takarar cinye kambun Sarauniyar Kyau ta wani wuri – sabida kishin da Musulunci yake dashi ga jinsin mata.

An yi mata masu tsananin kyau a tarihin daulolin Musulmi (har yanzu ana samu), amma sabida bin koyarwar Musulunci na za mu ga lafiyayyiyar Musulma tana tunƙaho cewa ba bu wacce ta kama ƙafar ta ta fannin kyau ba. Hasali ma, duk mun yarda cewa kyau abu ne mai zamani, kuma ba’a yin sa ga mace daya-tilo a fadin ƙasa ko Duniya. Sabida shi zuciya da idanu ne suke kallon sa, kowa kuma da tasa zuciyar.

A tsari na Addinin Islama, ba bu wata dama, ko daga ƙafa da aka yiwa mace (mai kyawun halitta) da ta fito domin nuna wa Duniya irin kyawun da Allah Yayi mata, ballantana har ace ‘wai’ an zabe ta a matsayin wacce tafi kowa kyau.

Annabi Muhammad (SAW) Ya fada mana cewa “mafi khadari daga cikin matekun ku, su ne wadanda suke bayyana kyawun/surar jikin su da mutanen da ba Muharraman su ba. Annabin rahama ya ce irin matayen nan, ba za su shiga Al-Jannah ba.

Annabi (SAW) Ya sake ba mu labari cewa “mafi soyuwa daga cikin matayen ku, sune masu tsoron Allah (masu hayayyafa). Sa’annan mafi khadari da shedancin cikin su, sune wadanda suke yin ‘Tabarruj’ da sunan nuna kyawun da Allah Yayi masu.”

Akwai kuma wadanda ake kira da Al-Mutakhayelat – wadanda suke yin kwarkwasa ko máde ga wadanda ba mazajen su na aure ba, to kai tsaye su Munafukai ne – kuma ba za su shiga Al-Jannah ba.

Babban abin takaicin a lamarin wannan yarinya, A’ishatu Garko, shine yadda kafafen yada labarai suke ta rubuta cewa wai “Yarinya Mai Hijabi Taci Gasar Sarauniyar Kyau Ta Najeriya” wanda ‘mudliqan’ cin zarafin Addinin Musulunci ne wannan.

Mene ne yasa za’a shigo da maganar “Hijabi” a lamarin Shaydan? Ko so suke yi sauran masu sanya Hijabi su dauka cewa abin kirki tayi? Kuma tsakani da Allah, wannan ‘scarf’ din shine Hijabi? Hotuna nawa ne ”Shatu Garo” din tayi ba bu Hijabi a jikin ta, sam?

Wai, yaya ma ake shiga takarar muƙamin Sarauniyar Kyawun; dame-dame ake dubawa a jikin su; ko kuma wace irin fitsara ake so mace ta ƙware kafin a ba ta? Ya kamata masu tace labaran gidajen jaridun Musulmi su san mene ne yaci karo da shari’a – wanda laifi ne fitar sa; da kuma wanda ba bu laifi fitar sa.

Mata nawa ne, wadanda kullum suna cikin Hijabi – amma sun fi wannan Garon kyawu a anguwannin mu da garuruwan mu? A taƙaice, ba kowane namiji ne (mai hankali) zai yarda cewa Shatu Garko ta fi matar sa, ko Budurwa sa kyau ba…musamman itama mai hankali ce.

Sabida da haka, Shatu Garko ta sani mu a wurin mu, itace Sarauniyar Munanan Najeriya – domin ko ni marubucin wannan saƙon na fi ta kyau.

Muhammad Bashir Ɗan Jarida ne ya rubuto daga Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet