Labarai
Mummunan Hatsarin mota ya kashe mutum takwas a Jihar Bauchi
Hatsarin mota ya yi ajalin aƙalla mutum takwas a Jihar Bauchi ranar Asabar.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗura a Bauchi, Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da kamfanin labarai na NAN a yau Lahadi.
A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ƙauyen Goltukurwa da ke kan titin Das zuwa Bauchi, inda ya ritsa da ƙaramar mota ƙirar Opel Vectra da kuma tifa ƙirar Mercedes Benz.
Kwamandan ya alaƙanta lamarin da yin lodi fiye da kima, yana mai cewa jami’ansu sun isa wurin cikin minti bakwai da faruwarsa.
Mutum tara ne hatsarin ya ritsa da su; maza biyu, mata shida da kuma yaro ƙarami, a cewarsa.
