Connect with us

Labarai

Siyasa A Yau: Rikicin Jam’iyya Ba Zai Karkatar Da Hankalinmu Wajen Kasa Bunkasa Jihar Ba- Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ranar Lahadi ya gana da ‘yan jam’iyyar APC masu biyayya ga bangaren sa domin duba rikicin da ke fuskantar jam’iyyar.

Solacebase ta tuna cewa wasu hukunce-hukunce guda biyu da wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta yanke, sun tabbatar da zaben mazabu da na kananan hukumomi da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta tare da amincewa da Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar a Kano.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar ta ce, Dakta Abdullahi Ganduje ya sanar da taron ne a gidan gwamnati, cewa, an kira su ne domin a sanar da su cewa akwai bukatar zaman lafiya a jam’iyyar.

Ganduje ya jaddada cewa, “Bai kamata mu ja baya ba saboda rikicin jam’iyyar da aka saba yi. Wannan al’ada ce ta tsarin dimokuradiyya. ”

“Yana da matukar muhimmanci kowa ya san cewa hazakarmu ta siyasa da gogewar siyasarmu ba za su bari rikicin kananan jam’iyya ya karkatar da hankalinmu wajen kasa bunkasa jiharmu ta Kano ba.

Abin da ke faruwa wani bangare ne na al’adun dimokuradiyya,” in ji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta Kudu da kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Ibrahim Hamisu Chidari da dan majalisar wakilai kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Alhasan Rurum, wadanda suka yi magana a madadin sauran ‘yan majalisar da ke goyon bayan bangaren sun tabbatar wa Gwamna Ganduje goyon baya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet