Connect with us

Labarai

An Sake Gano Wasu Gawarwakin Mutane A Karamar Hukumar Giwa

An sake gano wasu gawarwaki biyu biyo bayan wasu hare-hare da aka kai wasu kauyuka uku a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu ya kai 40.

‘Yan bindiga sun mamaye kauyukan ne tsakanin ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi inda suka bude wuta kan mutanen kauyen da ba su ji ba ba su gani ba.

‘Yan bindigar sun kuma kona gidaje da motoci da filayen noma a yayin harin da aka kai kauyukan uku – Kauran Fawa, Marke da Riheya.

Ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta ce gawarwakin da aka kwaso 38 ne amma kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels a ranar Litinin cewa an samu karin gawarwaki biyu.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike a kananan hukumomin da lamarin ya shafa.

A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da munanan abubuwan da suka faru a Kauran Fawa, Marke da Ruhiya da ke gundumar Idasu ta karamar hukumar Giwa, inda ya ce ya yi matukar bakin ciki da abun.

Buhari a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Kaduna da al’ummar kananan hukumomin da abin ya shafa.

Bugu da kari, ya kuma aike da ta’aziyyar al’ummar masarautar Zonkwa da iyalan Mai Martaba Nuhu Bature, Agwam Kajju bisa rasuwarsa.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Da yake jawabi, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun mayar da martani ga ‘yan ta’addan da ke kara fusata ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, suna wawure dukiyoyinsu da kona gidajensu da kuma kashe su ba gaira ba dalili.

Ya kuma kara nanata umarninsa ga shugabannin tsaro da na leken asiri da su yi duk abin da za su iya domin lalata sauran sassan ‘yan ta’adda.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwingrandpashabet güncel girişjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetgrandpashabetsahabetsahabetgrandpashabet güncel girişcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabet girişpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet