Connect with us

Labarai

Sojoji A Ƙasar Malesia Sun Raba Abinci Ga Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ya Hana Su Fita Daga Gidajensu

Sojojin Malaysia sun yi amfani da kwale-kwale a jiya Talata wajen rarraba abinci ga mutanen da suka makale a gidajensu bayan ambaliyar ruwa, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 14 tare da raba sama da 70,000 da muhallansu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kwanakin baya ne ya janyo ambaliya mafi muni da aka shafe shekaru da dama ana yi a fadin kasar a karshen mako, inda ta mamaye birane da kauyuka tare da yanke manyan tituna.

Selangor – jihar da ta fi kowacce wadata kuma mafi yawan jama’a, ta kewaye babban birnin Kuala Lumpur – na daya daga cikin yankunan da lamarin ya fi kamari.

A birnin Shah Alam, har yanzu wasu yankuna na karkashin ruwa a ranar talata, kuma sojoji a cikin kwale-kwale sun raba abinci ga mutanen da suka makale a gidajensu da matsugunan gwamnati.

Kartik Subramany ya tsere daga gidansa yayin da ambaliyar ruwa ta tashi, kuma ya nemi mafaka a wata makaranta na tsawon sa’o’i 48 kafin a kwashe shi da iyalinsa zuwa wani matsuguni.

“Gidana ya lalace gaba daya, motoci na biyu sun lalace,” dan shekaru 29 ya shaidawa AFP.

“Wadannan sune ambaliyar ruwa mafi muni a rayuwata. Gwamnatin tarayya ta gaza wa jama’a sosai – ta gaza a aikinta na farko na kare da kiyaye rayuka.”

Dubban jami’an agajin gaggawa da na soji ne aka shirya, sai dai masu suka sun ce bai isa ba, kuma masu sa kai sun shiga aikin samar da abinci da jiragen ruwa domin aikin ceto.

Haka kuma an samu rahoton an wawure manyan kantuna a wata unguwa mai tsananin zafi a unguwar Shah Alam.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet