Labarai
Gwamnatin Kano ta kori ma’aikatan da ta samu da takardun bogi
Hukumar da ke kula da al’amuran ma’aikata a Jihar Kano ta sanar da korar wasu ma’aikata guda huɗu da a ka same su da takardun karatu na ƙarya.
Shugaban hukumar, Bello Muhammad Ƙiru ne ya baiyana hakan a yau Alhamis bayan zaman aikin ƙara likkafar manyan maikata.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar, Samaila Garba Gwammaja, hukumar ta kuma daga likkafar ma’aikata 126.
Ya ce a cikin waɗanda a ka ƙarawa likkafar har da mataimakan daraktoci da ke kan matakin albashi na 15 zuwa matsayin daraktoci a mataki na 16, maikata 34 da ke mataki na 12 zuwa matsayin Mataimakin Darakta a mataki na15.
Ya ƙara da cewa sauran wadanda a ka ciyar da su gaba sun haɗa da wadanda su ke a matsakaicin matsayi da sauransu.
Kiru ya nuna farin cikin sa a bisa nasarar aikin daga likkafar ma’aikatan.
