Labarai
Gwamnatin Buhari za ta sake ɗiban matasa 4000 shirin N – Power
Ministar Ma’aikatar Jinkai da Cigaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i a Najeriya, Sadiya Umar Farouk ta sanar da cewa gwamnatin tarayya na shirin sake ɗaukar matasa dubu 400 a shirin N-Power.
Ministar ta yi sanarwar ne a Kano a jiya Laraba a gurin yaye ƴan rukunin C1 na N-Knowledge a jihar Kano.
Ta ƙara da cewa adadin wani ɓangare ne na matasa miliyan ɗaya da shugaban ƙasa ya sahale a ɗauka.
Ta ce matasa dubu 510 ne su ka amfana da shirin a rukunin C 1, inda ta ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba za a fara rukunin C 2.
Haka kuma Sadiya ta yi bayani cewa shi shirin na N- Knowledge zai taimakawa matasa ne wajen gogar da su kan harkar aikin ofis, ƙirƙire – ƙirƙire da kuma harkokin kasuwanci a gida Najeriya da ma ƙasashen waje.
Ministar, wacce ta samu wakilcin Mataimakin Darakta a ma’aikatar, Muhammad Sambo, ta ce matasa dubu uku ne da ga yankin Arewa-Maso-Yamma su ka samu horo kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a rukunin na C1.
A ƙarshe ta yi kira ga matasan da su ka amfana da su yi ƙoƙari su yi aiki da horon da su ka samu domin bunƙasa tattalin arzikin su a rayuwa.
