Addini
Wani Limamin Coci zai shafe shekaru 21 a gidan yari sakamakon aikata laifin cin zarafi
Wata kotu a Rasha ta ɗaure wani tsohon limamin cocin Orthodox ta addinin gargajiya na Kirista na tsawon shekaru 21 a gidan yari kan laifin cin zarafin yara.
An bayyana cewa ya karɓi mallakar yara kimanin 70.
An samu Nikolai Stremsky da laifin yi wa yara da dama fyaɗe da kuma aikata wasu laifuka a cikin cocinsa da ke yankin Urals a kudu maso yammacin Rasha.
An yi la’akari da Stremsky a matsayin mafi girma a Rasha kuma ya samu lambar yabo ta ƙasa.
An cire shi daga muƙaminsa na malamin coci da kuma tuɓe masa darajarsa.
Stremsky da matarsa suna da wani gidan reno tun a 199o, inda suke mallakar yara daga daga gidan marayu a yankin Saraktash, yawancin yaran daga cikin 70 sun girma.
A 2019 aka kama shi kuma aka gudanar da bincike kan zargin cin zarafin yara bakwai, zargin da ya musanta a matsayin ɓatanci.
