Labarai
Yadda Ƴan sanda su ka cafke matashin da ya yi ƙaryar an yi garkuwa da shi a Kano
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama wani matashi, mai suna Hayatu Musa, wanda ya yi ƙaryar cewa ƴan ta’adda sun yi garkuwa da shi domin mahaifinsa ya bada kuɗin fansa.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya shaidawa manema labarai a jiya Alhamis a Kano.
A cewar Koyawa, matashin, ɗan Ƙaramar Hukumar Madobi, ya nuna ya na buƙatar kuɗi ne a wajen mahaifinsa, shine ya biyo ta sigar cewa an yi garkuwa da shi domin ya samu cikin sauki.
Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Kiyawa ya ce matashin ya makale murya ne sai ya kira ƙaninsa ya ke shaida masa cewa an sace yayansa sabo da haka a na neman kuɗin fansa naira dubu 100.
Ya ƙara da cewa bayan sun gama ciniki ne shine a ka tsaya a dubu 70, in da ya ce a wajen biyan kuɗin fansar ne a ka cafke Musa ɗin.
Shi da kansa Musa ɗin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya ji bashi da kuɗi ne shine ya yi amfani da wannan hanya don ya samu kuɗi da ga mahaifinsa.
A cewar sa, “na ji ina buƙatar kuɗi ne kuma na san da wuya na samu a wajen baba na shine na tafi wani gari wai shi Kanwa.
“Bayan na je shine na shiga jeji na makale murya na kira kanina na ke gaya masa an yi garkuwa da yayansa, shi kuma bai san ni ba ne.
“Gaskiya babu wanda ya sa ni na yi wannan abun, kawai dai ni na kirkira da kaina,” inji Musa.
Shima mahaifin sa ya ce bayan an kira shi ta wayar kanin Musa ɗin, sai su ka yi ciniki da ga naira dubu 100 zuwa dubu 79 kuma duk bai san ɗan sa ba ne.
“Bayan ya kira da daddare, sai bai sake kira ba sai washegari da safe ya ce a bashi dubu 100 na ce bani da shi. Bayan nan dai mu ka yi ciniki a ka tsaya a dubu 70.
“To a wajen kai kuɗin ne dubun sa ta cika kuma gaskiya ban ji daɗin abin da ya yi ba,” in ji mahaifin Musa.
