Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Tabbatar Da Naɗin Sabon Babban Alƙali

Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da nadin sabon babban alkali, shugaban kotun daukaka kara na shari’a da kuma shugaban kotun daukaka kara na gargajiya.

Gwamna Ahmadu Fintiri ya kaddamar da shugabannin kotunan a ranar Juma’a a Yola.

An kaddamar da Justice Nathan Musa, da Usman Girei da Peter Wajilda a matsayin alkalin alkalan Adamawa, Grand Khadi, kotun daukaka kara ta shari’a da kuma shugaban kotun daukaka kara na gargajiya.

Gwamnan ya bukaci wadanda aka nada da su yi duk abin da za su iya don inganta tsarin tabbatar da adalci a jihar.

“Aikin da ke gaban ku ba shi da sauki, duk da haka, ina rokon ku da ku jajirce wajen mayar da bangaren shari’a na gwamnati ya zama na musamman kamar yadda ake tsammani,” in ji Fintiri.

Da yake mayar da martani a madadin wadanda aka nada, Mai shari’a Musa ya tabbatar da cewa za su inganta tsarin doka a jihar tare da kare muradun kowa da kowa.

Babban Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, Afraimu Jingi, ya rantsar da sabon alkalin alkalai tare da rantsar da sabon Alkalin, wanda shi kuma ya gudanar da rantsuwar a Girei da Wajilda. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet