Labarai
Matsalar Tsaro: Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani Sarki a jihar Filato
A yau Lahadi ne ƴan bindiga su ka ɗauke Charles Mato, mai riƙe da sarautar Sum Pyem kuma Sarkin Gindiri a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.
Mejo Ishaku Takwa, kakakin rundunar sojoji da ke yunƙurin sake da zaman lafiya a jihar, wacce a turance a ke kira da ‘Operation Safe Haven’, shi ya tabbatar da afukuwar harin.
Ya tabbatarwa manema labarai a Jos cewa ƴan bindiga sun yi awon-gaba da Sarkin a gidansa da ke Gindiri.
Amma ya ce an haɗa dakaru da ga rundunar haɗin gwiwa domin su fara bincike da kuma kuɓutar da Sarkin.
Ya baiyana cewa tuni dakarun su ka fara bin sawun ƴan ta’addan da su ka yi garkuwa da Sarkin.
