Labarai
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Karamar Hukumar Mangu
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Mista Charles Mato, Sum Pyem, kuma basaraken Gindri, a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato ranar Lahadi.
Maj. Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na Ofureshin (OPSH), a rundunar soji da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da sace mutanen.
Ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi a Jos cewa an yi garkuwa da Mato ne daga gidansa da ke Gindiri.
Ya ce an tattara dakarun da ke aiki a yankin domin gudanar da bincike domin ceto.
“Dakarun OPSH da ke Gyambus a Mangu an tattaro su zuwa yankin Suna kan hanyar masu garkuwa da mutane,” in ji Takwa. (NAN)
