Connect with us

Labarai

Wasu Ƴan Gida Daya Yara Biyu Sun Nitse A Kogin Asa Yayin Wanka Ilorin

Wani bala’i ya afku a Ilorin, babban birnin jihar Kwara yayin da wasu ‘yan gida Mutu biyu suka nutse a cikin kogin Asa kuma jami’an kashe gobara na jihar Kwara suka tsinto gawarwakinsu a yammacin ranar Juma’a.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce ta kwaso wasu yara Damilare mai shekaru 12 da kuma Kamaldeen mai shekaru 14 daga kogin Asa daura da unguwar ‘Laola Salasi Street Mubo llorin da misalin karfe 5 na yammacin ranar Juma’a.

Yaran biyu a cewar hukumar kashe gobara, an gano gawarwakinsu daga kogin.

Majiyoyi sun ce yaran tare da abokan wasansu sun tafi bakin kogi da yammacin ranar Juma’a domin yin nishadin wanka kamar yadda suka saba.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban yada labarai Hassan Adekunle kuma ta mika wa manema labarai a Ilorin a daren Juma’a.

Sanarwar ta ce; “Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta samo wasu yara maza biyu, Damilare mai shekaru 12 da kuma Kamaldeen mai shekaru 14 a kogin Asa ‘Laola Salasi Street Mubo area ilorin, ranar 31 ga watan Disambar 2021.

“Wannan mummunan al’amari ya faru ne da yammacin ranar Juma’a da misalin karfe 16:36 (04:36 na yamma), kwatsam wani Alhaji Eleja ya kira Brigade zuwa wurin da lamarin ya faru.

“Duk da haka, abin takaici ne yadda ‘yan kwana-kwana suka tsinto gawarwakin mutanen biyu (Kamaldeen da Damilare) daga kogin.

“Wadanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga harabar ile-laru, unguwar sabo-line Ilorin tare da abokan aikinsu sun je yin iyo a kogin Asa-River kafin daga bisani suka nutse a cikin kogin, muka mika gawarsu ga mahaifinsu, Alhaji Jamiu kafin mu bar wurin da abun ya faru.

“Saboda haka, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade Olumuyiwa ya bukaci ‘yan kasa musamman iyaye da malamai da su cigaba da sanya ido kan motsin ‘ya’yansu musamman a wannan lokacin na hutu domin gujewa irin wannan mummunan lamari da zai biyo baya”, in ji sanarwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet