Connect with us

Featured

LABARINA: Aminu Saira, Nafisa, Nuhu Abdullahi da Kannywood

Watakila idan nace kasuwar Hausa ta mutu ban yi kuskure ba, amma Kuma zata iya kasance wa nine ban fahimci halin da kasuwar take ciki ba, amma dai kasuwar fina finan Hausa tana cikin bukatar agaji da shugabanci na gari da kuma hadin kai a tsakanin waɗanda suke cikin masana’antar ta Kannywood.

Shirye shirye masu dogon zango (Series films) sune suka kasance abinda masana’antar Kannywood ta rike a matsayin Wanda zai rike harkar saboda masu kallo sun karkata da kallon shiri mai dogon zango.

Tun farkon fara shirin LABARINA ya karbu a wajen al’umma musamman masu son kallon shirye shiryen Hausa, saboda yadda ake labarin film din a shafukan sada zumunta da Kuma shi kansa yadda marubucin ya tsara labarin.

Tun daga lokacin da aka fara tallan film din na fara jiran ranar da za’a fara haskawa, hakan yasa tun daga ranar da aka fara shirin har yau babu abinda ya wuce ni a cikin shirin Kuma nayi sharhi akan shirin tun farko-farko, kafin in daina saboda dalili na kashin kaina.

Masu bibiyar Shirin sun dade da samun labarin cewa Nafisa Abdullahi zata daina fitowa a cikin shirin, tun kafin ta fitar da sanarwar data fitar a jiya.

Fitar Nafisa ya haifar da gagarumin gibi a cikin shirin duba da yadda aka gina labarin a kanta Kuma babu yadda shirin zai ci gaba ba tare da haska taba, Kusan kashi 70 cikin 100 na waɗanda suke cikin Shirin LABARINA suna da alaka da labarin Nafisa wanda hakan yasa ta zama jagora a film din.

Haka Shima Nuhu Abdullahi, Wanda Shima yana da tasiri sosai a cikin shirin, saboda daraktan shirin sai daya fara fitar dashi daga cikin Labarin, bayan yabar gida saboda rashin sanin asalinsa, Amma aka sake dawo dashi cikin rayuwar Sumayya saboda Labarin Sumayya ba zai cika ba sai da Mahmoud, Amma daga baya darakta ya fitar dashi ta hanyar kasheshi.

Amma muyi duba kan Nafisa da Nuhu Abdullahi kafin fara shirin LABARINA.

a tsarin Kannywood, jaruman masana’antar suna da Daraja guda uku Kamar yadda ni nake gani, akwai Wanda jarumi ne Kuma dole Sai dashi, wato idan kanason film dinka ya samu Kasuwa kana bukatar su. Akwai waɗanda Babu yabo Babu fallasa wato yan tsakiya sai kuma waɗanda Yan ciko ne.

Sannan kafin shirin LABARINA duk Wanda yake bibiyar fina finan Hausa yasan Nafisa ta fita daga cikin jaruman da suke kan ganiyar su, wato Ina nufin an samu matasa masu tasowa. Shirin LABARINA ne ya dawo da Nafisa kan ganiyar ta Kuma ta dawo da sharafinta.

Bayan fara LABARINA Nafisa ta samu talla da kamfanin Pepsi, idan banyi kuskure ba, sannan ta bude kamfani Kamar yadda ta bayyana bugu da Kari hotunan ta suka dawo shafukan sada zumunta da jaridu.

Nuhu Abdullahi yana cikin yan babu yabo babu fallasa, wato jarumi ne Wanda idan Babu shi a cikin film zai karbu Kuma LABARINA ya dawo da martabar sa a cikin Kannywood.

Me yasa suka fita?

Kamar yadda Nafisa ta bayyana dalilan ta waɗanda sune suka saka ta yanke hukunci fita daga cikin shirin, har yanzu bamu ji dalilin da yasa Nuhu Abdullahi ya fita ba, daga bakinsa ko Kuma daga wajen daraktan film din.

Dole ne in girmama dalilansu, amma fa kada su manta cewa sun shiga wani layi da al’umma suke kallon su a matsayin masu debe musu kewa kuma sun dakko wani aiki wanda masu kallo suke bibiyar su har ake bata lokaci ana kallon su sannan ayi sharhi akan shirin LABARINA duka saboda su.

Sun Kai wani mataki a cikin shirin LABARINA Wanda dole mai kallo yana bukatar su domin ganin yadda labarin zaizo karshe.

Tabbas abinda sukayi ba zaiyi wa mai kallo dadi ba idan har sun yadda cewa domin al’umma sukeyi to yakamata dasu da daraktan film din suyi hakuri su kammala aikin da suka dakko domin kada su rasa Daraja da girmamawa tare da goyon baya daga wajen masu kallo. Sannan Suma watakila suna da burin yin film nasu na kashin kansu ( Daman Nafisa tanayin nata) wannan matakin da suka dauka zai iya shafar kasuwar su ta gaba (bana fatan haka).

Aminu Saira

A Shekarun baya bana tsayawa in Kalli kowanne irin film idan har ba Aminu Saira ne yayi ba saboda yadda ya iya bayar da umarni da Kuma kawo labari mai sosa zuciya.

Hakan yasa na sake amincewa dashi a wannan lokacin tunda naga shine daraktan film din, saboda na gama yarda da aikinsa.

Kuma a cikin shirin idan mai kallo bai manta ba ai ya canja mahaifin Presido, da farko Ibrahim Mandawari ne mahaifin Presido Amma daga baya aka canja shi saboda wani dalili da Saira bai bayyana ba. Yadda na yarda da iya aikin Saira, nayi zaton zaiyi wani abu domin ganin fitar Mahmoud daga cikin Shirin bata taba Darajar Labarin ba, sai dai kawai ya yanke hukunci ya cire shi saboda rashin daidaita kwangila (idan ita suke kullawa).

Akwai fina finai da dama da akayi kuma aka canja jarumai ba tare da an samu irin wannan matsalar ba kuma babu abinda ya canja saboda shi mai kallo Labari yake bibiya ba jarumai ba (Amma Suma jaruman suna taka babbar gudunmawa wajen karbuwar film).

Saira tabbas ya samu matsala kuma yana da damar daukar duk wani mataki wanda yake ganin yafi masa kyau amma yana bukatar ci gaba da tafiya da masu bibiyar sa saboda yadda aka yarda da aikinsa.

Kannywood

Wannan abinda ya faru a cikin shirin LABARINA barazana ce ga Kannywood saboda nan gaba za’a iya samun wasu jaruman su aikata abinda ya faru. An nunawa jarumai masu tasowa hanyar yin bore a lokacin da suka ga cewa dole sai anyi dasu a harkar.

Fina finai masu dogon zango sune suka ragewa Kannywood Kuma tun kafin suyi nisa sun fara daukar hanyar lalata harkar.

Yanzu yan Kannywood sun zama Yan siyasa, sun koma tallan Yan takara, daga wajen wannan dan siyasar sai wajen wannan, har Kar fim din ta fara tsayawa, sannan sun fara Dawowa ta hanyar series fim Amma wannan matakin da suka fara dauka tabbas Babu inda za suje.

Abba Gwale, ɗan jarida ne ya rubuto daga Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet