Addini
Bashir Tofa cikakken ɗan kishin Najeriya ne – Atiku
Tsohon mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya miƙa ta’aziyyar rasuwar tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar Bashir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin “cikakken ɗan kishin ƙasa”.
Sanarwar ta ƙara da cewa Atiku Abubakar ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan sa sannan ya bai wa iyalai da abokansa haƙurin rashinsa. ” A kowanne lokaci yakan bada gudummawa da shawara akan al’umara da suka shafi wannan kasa. Mutum ne mai ra’ayin da babu son zuciya. Ameen,”.
“Tabbas wannan babban rashi ne. Ina Adduar Ubangiji Allah ya jikansa ya yafe masa. Allah ya bashi gidan Aljanna. Ameen”, in ji Atiku Abubakar
Bashir Othman Tofa ya rasu da asubahin Litinin yana da shekara 74 bayan ya sha fama da jinya kuma an yi jana’izarsa a birnin Kano.
