Connect with us

Labarai

Katsinawa da ƴan Najeriya za su dara a shekarar 2022 – Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewar al’ummar jihar Katsina da ma Najeriya baki daya za su ji daɗi a shekarar 2022.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon sa na bikin sabuwar shekara da Darakta Janar na yada labaran sa, Abdu Labaran ya fitar a madadin sa.

A cewar Gwamnan, shekarar 2022 ta daban ce domin kuwa ita ce shekara ta karshe da gwamnatin Shugaba Buhari za ta kammala da wasu gwamnatocin jihohi da dama ciki hadda ta Katsina da yake jagoranta.

Masari ya ƙara da cewa a shekarar ta 2022 gwamnatin sa za ta tabbatar da an murkushe ayyukan ta’addancin da jihar ta ke fama da shi.

Hakazalika Gwamnan ya ce duk da matsalar tattalin arziki da cutar Korona ta jawo wa duniya ciki har da Katsina, yana da yakinin cewa jihar za ta warware a shekarar ta 2022 ta kuma shimfida wa al’umma ayyukan more rayuwa.

Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya kamar Zamfara da Kaduna da ke fama da matsalolin tsaro da suka danganci fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

Yankuna da dama na jihar na ganin hare-hare a kai a kai inda ƴan bindiga ke aukawa ƙauyuka su kashe mutane sannan su yi awon gaba da mata da ƙananan yara tare da satar dabbobi.

Daga ƙarshe gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya da su haɗa kan su domin samun cigaba mai dorewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet