Labarai
Cutar Korona ta kama shugaban ƙasar Mozambique da matarsa
Shugaba Filipe Nyusi da matarsa sun killace kansuImage caption: Shugaba Filipe Nyusi da matarsa sun killace kansu
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi da uwar gidansa Isaura Nyusi gwaji ya tabbatar da sunkamu da korona inda suka killace kansu.
Sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta ce Mista Nyusi da matarsa sun amince su killace kansu kamar yadda ka’idojin ƙasa kan matakan korona suka tanada, duk da cewa ba su nuna alamomin cutar ba.
Ta ce sun amince su yi gwaji bayan “abubuwa da dama da muka yi akwanakin da suka gabata.
Korona na ƙara bazuwa a kwanakin nan
Mutum 193,000 suka kamu da cutar a Mozambique, yayin da ta kashe 2,031 yayin da mutum 158,680.
