Addini
Gwamnan Jihar Kogi Ya Karɓi Bakuncin Shugabannin Darikar Tijjaniya
Gwamna Yahaya Bello na Kogi a ranar Alhamis a Lokoja ya karbi bakuncin Mai Martaba Sheikh Ibrahim Niasse, babban Khalifan darikar Ansarideen (Attijaniya) na duk duniya, yayin da jihar ke karbar bakuncin Maulidin darikar na Duniya karo na hudu a Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron, mai taken “mafitar annabci ga tambayoyin bil’adama”, yana gudana a Lokoja daga ranar 6 ga Janairu zuwa 8 ga Janairu.
NAN ta ruwaito cewa a cikin tawagar akwai tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne shugaban darikar Ansarideen (Attijaniya) ta Najeriya, da sauran malaman addinin Islama.
Darikar Ansariddeen (Attijaniyya) karkashin jagorancin Sheikh Niasse ce ta shirya taron Maulidi wanda aka yi don girmama Manzon Allah (SAW).
Haka kuma ana sa ran halartar malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na kasashen duniya tare da gabatar da laccoci da dama da suka shafi koyarwar Manzon Allah (SAW) kamar yadda ya shafi wannan zamani.
Taron dai zai hada da ziyartan majinyata da yi wa majinyata addu’a a asibitoci daban-daban na jihar, liyafar cin abinci ta musamman don girmama Manzon Allah (SAW).
Haka kuma za a yi Zikirin Juma’at, wacce aka fi sani da ibadar yabo ta Juma’a, wanda za a yi a babban masallacin Juma’a na Lokoja.
