Addini
Shahararran Malamin Addinin Musulinci Dr Ahmad Bamba BUK Ya Rasu
Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya rasu
KakakiHausa ta ruwaito cewa Dr. Ahmad Ibrahim Bamba wanda aka fi sani da Dr Ahmad BUK ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya.
Dan sa Ahmad Muhammad Ahmad ya sanar da rasuwar mahaifinsa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a ranar Juma’a.
Ya ce za a yi jana’izar marigayin a masallacin Darul Hadith, Tudun Yola, cikin birnin Kano da misalin karfe 1:30 na rana.
Marigayi Dr. Ahmad ya kasance malami a Sashen Larabci da ke BUK kafin ya yi murabus ya shiga aikin wa’azin Musulunci gaba daya.
