Ilimi
Gwamnatin Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da PRNigeria Don Horas Da Ƴan Jaridu
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyar ta na hada gwiwa da kamfanin PRNigeria Center Kano, reshen kamfanin IMPR, domin horar da jami’an yada labaransu a ma’aikatu da hukumomi da kananan hukumomi 44.
Kwamishinan yada labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da wanda ya kafa cibiyar PRNigeria, Malam Yushau Shuaib da tawagarsa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

“Na yi matukar farin ciki ya kuma burge ni sosai domin ina ganin irin wadannan cibiyoyi ne da nake bukata musamman don horar da abokan aikinmu a harkar yada labarai, la’akari da cewa batun fasaha ya zama abin tattaunawa sosai har ya zuwa yanzu aikin jarida ya yadu a duk duniya,” in ji shi.
Mallam Garba ya tabbatarwa da tawagar kamfanin PRNigeria a shirye ya ke ya yi aiki da su domin jami’an yada labarai na bukatar horo da sake horas da su domin cim ma fasahar zamani da sabbin tsare-tsare a fannin hulda da jama’a da aikin jarida.
“Ina so in tabbatar muku kamar yadda na fada a ziyararku ta karshe, a shirye muke mu yi hadin gwiwa da ku a kowane lokaci domin sadarwa kamar yadda yake a yau musamman a fannin aikin jarida da hulda da jama’a, mutum yana bukatar horo sosai da sake farfado da tattalin arzikin kasa. Akwai fasahohin zamani da yawa, akwai sabbin tsare-tsare da yawa dangane da dabarun sadarwa a Najeriya da ma duniya baki daya,” in ji Garba.
Mallam Garba ya kuma shaidawa tawagar PRNigeria cewa zai tattauna akan horon hulda da jama’a tare da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Murtala Sule Garo, domin ganin yadda zasu samu saukin horon a matakin kananan hukumomin.
“Zan tattauna da kwamishinan kananan hukumomi a hukumance saboda muna da kudaden horarwa a matakin kananan hukumomi, shi abokin aikina ne sosai. Zan tattauna da shi, in ga yadda muke saukaka horo a matakin kananan hukumomi.
” A kowace karamar hukumar mu 44, muna da jami’an yada labarai, mataimakan jami’an yada labarai da masu daukar hoto. Za mu yi farin cikin ɗaukar shirye-shiryen horo a cikin PRNigeria, la’akari da ƙididdige kayan aikin ku. Za mu yi aiki kan yiwuwar bayyana shirin a hukumance nan ba da dadewa ba,” inji Malam Garba.
A nasa bangaren, Alhaji Yushau Shuaib, ya baiwa gwamnatin jihar Kano tabbacin horar da jami’an yada labarai masu tasiri a duk lokacin da aka samu dama.
Ya zayyana nasarori da ayyukan da cibiyar PRNigeria da ke Abuja da Kano ta samu a fannonin karawa juna ilimi da horar da ‘yan jarida da jami’an hulda da jama’a da kwararru da sauransu.
Ya kuma kara da cewa Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) da Ma’aikatar Sadarwa da tattalin arziki na zamani sun taimaka sosai wajen samar da na’urori na zamani ga wasu shirye-shirye na inganta karfin cibiyoyin.
By PRNigeria
