Addini
Gwamnatin Kano ta shirya taron addu’o’in zaman lafiya a Najeriya
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta shirya wani taron gangamin addu’a akan samun zaman lafiya da ƙaruwar arziki.
An dai shirya wannan gangami karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shugabannin addininai musamman na ɓangaren ɗariƙar Tijjaniyya, domin yin addu’a don shawo kan matsalar tsaro da ta yiwa ƙasar nan dabaibayi.
Haka kuma manyan masu fada-a-ji na gwamnatin Kano ne da dama suka halarci taron addu’ar, inda da yawa suka nuna damuwa dangane da halin da ake ciki a arewacin Najeriya.
Taron addu’ar wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, ya samu halarcin shugaban ɗariƙar Tijjaniyya na duniya Sheikh Ali Bel Arabi da Sheikh Dahiru Usman Bauchi da sauran Malamai.
