Connect with us

Labarai

Wasu Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 60 A Harin Kananan Hukumomi 2 Na Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kashe sama da mutane sittin a cikin al’ummar Zamfara biyar a wani sabon hari da suka kai a jihar.

Al’ummar su ne Kurfa Danya, Kurfa Magaji, Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka. Kauyukan da abin ya shafa al’ummomi ne da ke makwabtaka da su.

‘Yan bindigar sun far wa jama’a da yawa akan babura suna harbin jama’a da dama, lamarin da ya tilastawa mata da kananan yara yin gudu domin tsira da rayukansu.

TVCNEWS ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan ne da daddare a kan babura da yawa. Haka kuma sun kona gidaje da kayayakin abinci da sauran kayayyaki masu daraja

Kwamishinan yada labarai na Jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya shafa ba.

Ya kara da cewa dakarun sojin Najeriya ne suka kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar yayin da suka amsa kiran da jama’ar yankin suka yi musu.

Dosara ya lura cewa gwamnatin jihar na aiki tukuru tare da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa dukkanin al’ummomin da ke fama da rikici sun dawo da zaman lafiya mai dorewa.

Kokarin jin ta bakin hukumomin ‘yan sanda game da harin bai haifar da da mai ido ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet