Labarai
Hukumar FRSC Za Ta Fara Kama Masu Motoci Marasa Na’ura
Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta Kasa FRSC, Boboye Oyeyemi ya jajantawa iyalai da wadanda suka mutu a hadarin mota a ranar Alhamis da ta gabata a kusa da Makarantar Bagauda Law, kan hanyar Kano zuwa Zariya, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 19.
Ya kuma umurci kwamandojinsa da su kama masu ababen hawa da suka kasa sanya na’urar da ke ragee gudun wuce sa’a.
Oyeyemi ya ce an ba da umarnin ne domin tabbatar da aiwatar da umarnin shugaban kasa na shekarar 2016 kan sanya na’urorin da za su rage gudu ta motocin ‘yan kasuwa a fadin kasar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in kula da harkokin ilimi na hukumar FRSC Bisi Kazeem ya fitar ranar Asabar mai taken ‘Hukumar ta jajantawa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su a hanyar Kano zuwa Zariya.
Sanarwar ta ce ya umarci jami’ai da kwamandojin da su kara tsaurara matakan dakile kayyade saurin gudu.
‘’Shugaban rundunar ya bayyana damuwarsa kan asarar rayuka masu daraja, inda ya ce rage hadurran da ke da alaka da gudu na daya daga cikin tsare-tsaren da rundunar ta yi niyyar cimma a wannan shekara, don haka ne aka yanke shawarar dakile motocin ‘yan kasuwa da suka ki bin tsarin manufar takaita saurin na’urar,” in ji sanarwar.
“Yayin da yake jajantawa iyalan mamacin da sauran wadanda abin ya shafa, Oyeyemi ya bayyana cewa kawar da hadarurrukan da suka shafi gudu daga manyan tituna shine babban abin da ya fi mayar da hankali a kai tun hawansa ofis a matsayin shugaban hukumar.”
”Rundunar ta ci gaba da aiwatar da duk wani alhaki da jajircewa akan umarnin shugaban kasa kan rage gudun wuce sa’a; don haka ne rundunar ta fitar da tsare-tsare da dabaru da dama da suka hada da sanya na’urar da za ta rage gudun wacce sa’a, inda ta fara da motocin kasuwanci”.
“A matsayinmu na jagorar hukumar kula da kiyaye hadurra da zirga-zirgar ababen hawa, za mu ci gaba da amfani da dabarar tura kayan aiki da na wayar da kan jama’a da ma’aikata don tabbatar da cewa masu amfani da hanyar sun waye da kyau da kuma duba lafiyar kowa.”
