Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari Ya Nada Kakakin Majalisar Gbajabiamila Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya A Gasar AFCON

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya nada Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya jagoranci tawagar Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka fara ranar Lahadi a Kamaru.

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa Gbajabiamila mai kwanan wata 6 ga watan Janairu, 2022, wadda wakilinmu ya samu a ranar Lahadi.

Wasikar mai dauke da Lamba FMYSD/FEAD/FED/NFF/GR/CON/T/20, an yi mata lakabi da ‘Tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka (AFCON) na 2021 a Kamaru daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, 2022.

Ya kara da cewa, “Abin farin ciki ne na isar da amincewar mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na nadin da ka yi a matsayin jagoran tawagar gwamnatin tarayya, kana jagorantar tawagar ‘yan wasan Najeriya da za su halarci gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a birnin Yaounde na kasar Kamaru daga karo na 9 janairu zuwa 6 ga Fabrairu 2022.

“Tawagar za ta isar da sakon fatan alheri na shugaban kasa ga Super Eagles ta Najeriya, wanda zai kasance mai kara kuzari da kuma kara nuna goyon baya da jajircewar gwamnatin tarayya ga kungiyar a lokacin gasar.

“An shirya gudanar da wasannin matakin rukuni na Super Eagles a garin Garoua na kasar Kamaru, inda aka fitar da Najeriya a rukunin D tare da Egypt, Sudan, Guinea-Bissau a ranakun 11, 15 da 19 ga Janairu, 2022. bi da bi.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet