Connect with us

Kasuwanci

Kanawa Murna Har Kunne: Ƴan adaidaita-sahu sun janye yajin aiki a Kano

Matuƙa baburan adaidaita-sahu sun janye yajin aikin da su ka fara shi tun a ranar Litinin.

Ƴan adaidaita-sahun sun tsunduma yajin aiki ne domin nuna rashin goyon bayan su akan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,500 domin sabunta lambar rijista.

Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karɓar kuɗaɗen haraji barkatai a hannun su, musamman ma naira 100 da su ke biya kullum, inda har ranar Lahadi ma sai sun biya, duk da cewa ma’aikatan karɓar harajin ba sa fitowa a ranar.

Sai dai kuma a wata ganawa ta tsawon awanni uku da Shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ya yi, tare da lauyoyin ƙungiyoyin ƴan adaidaita-sahun, Barista Abba Hikima da Barista Muhammad Dalhatu, an cimma matsaya tsakanin ɓangarori biyun.

Bayan ganawar ne, sai dukkan ɓangarorin su ka kira taron manema labarai, inda a nan ne su ka sanar da cewa an janye yakin aikin.

Sun kuma nuna cewa matuƙa baburan adaidaita-sahun su fito su ci gaba da aiki a gobe Alhamis, bisa doron doka da oda.

Sun kuma baiyana cewa batun N8,500 na sabunta lambar rijista, za a duba shi, inda Dan-Agundi ya ce zai tuntubi gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje don ganin an rage farashin, ko kuma a bar su su biya a tsitstsinke.

Ya kuma ci alwashin samun kyakkyawar alaƙa tsakanin jami’an KAROTA da matuƙa adaidaita-sahun.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet