Addini
Siyasa Ba Da Gaba Ba: Ganduje Da Abdullahi Abbas Sun Kaiwa Danzago Ziyarar Ta’aziyya
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da shugaban jam’iyyar APC ɓangaren Gwamnati, Abdullahi Abbas sun kaiwa Alhaji Ahmadu Haruna Zago ziyarar ta’aziyyar rashin ɗan uwansa Shuaibu Zago da ya rasu a daren jiya.
Gwamna Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnatin Kano zuwa gidan Alhaji Ahmadu Haruna Zago da ke yankin unguwar Kurna da yankin ƙaramar hukumar Dala
Ahmadu Haruna Zago dai shi ke riƙe da muƙamin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaron abinci, haka kuma shi ne shugaban jam’iyyar APC na Kano ɓangaren tsohon gwamnan Malam Ibrahim Shekarau.
