Labarai
Majalisar Wakilai Za Ta Sake Gabatar Da Kudurin Dokar Gyara Dokar Zaɓe
Majalisar wakilai za ta sake gabatar da kudurin dokar gyara dokar zabe a zauren majalisar a ranar Laraba.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana haka a lokacin da yake maraba da abokan aikinsa zuwa harkokin majalisa a shekarar 2022.
Shugaban majalisar ya kuma nuna damuwarsa kan kura-kuran da ake zargin na cikin kudirin da aka aika wa shugaban kasa domin amincewa, yana mai dagewa da cewa wata kila an buga wani salo na daban.
Ya kuma ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa dokar gyaran kundin tsarin mulki za ta kasance a shirye domin gudanar da zaman majalisar dokokin jihohi kafin karshen watan Fabrairu.
