Labarai
Rundunar Ƴan Sanda A Jihar Neja Ta Tabbatar Da Yin Garkuwa Da Mutane 15 A Kulho
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da yin garkuwa da mutane 15 a garin Kulho da ke karamar hukumar Mashegu a jihar.
Hukumomin yankin sun ce ‘yan bindigar sun shigo ta garin Ibbi ne a wani kauye da ke kusa inda suka yi awon gaba da mutanen.
Hakazalika wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun shiga kauyen Mashegu ta yankin Jigawa a Mashegu inda suka yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba, yayin da suka fasa wani shagon sayar da kayayyaki a kauyen Kawo.
Idan dai za a iya tunawa a watan Nuwambar 2021 wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Maza kuka da kuma kauyen Adogon mallam da ke karamar hukumar Mashegu inda suka kashe mutane 16 da 17 a wasu hare-hare guda biyu.
