Addini
Dalilin Da Yasa Mutane Suna Karatun Amma Babu Dabi’u Masu Kyau
Babban ladabin da ya kamata a fara kula da shi yayin karanta Alkur’ani mai girma shi ne a san cewa Alkur’ani magance ta Allah madaukakin Sarki, kuma ba wai Allah yayi ta ne kawai ba sai dan ka fahimci abun da ayoyin suke fada, wanda wannan yake wajabta Musulmi ya san ilimin Larabci.
Sheikh Malam Abdullahi Uwais Abba Limanci ne ya bayyana haka a zantawarsa da Jaridar KakakiHausa a wajen saukar karatun Alkur’ani mai girma na makarantar Adam Mai Agogo Islamiyya da ke sharada phase 1 a Kano.
Sheikh Malam Uwais ya ce idan da tinani ya kamata idan mutum yana karatun Alkur’ani ya zama ya tsarkake zuciya da tufafi domin yana gaban Mal’iku ne a duk lokacin da yake karatun, kuma su kansu Malaman Makarantar su bar ladubban musulinci ko Malama wannan shi yasa ana karatun amma kamar ba’a yi dabi’unmu basa nunawa.
Malam Uwais ya ce daya daga cikin dalilan da yasa Matasa basa mayarr da hankali wajen neman ilimi shi ne an ruguza rayuwar Matasanmu, wanda a da Kano gari ne na noma da kasuwanci yanzu an rasa mana al’amura duk yanzu an doramu mun bar igoya mun kama zare ko ma iska.
Ya ce babbar dabi’ar da ya kamata ga mai karatun Alkur’ani ya kasance shi ya zama duk inda aka ganshi ya zama fassara ce ta Alkur’ani ba wai fassara Alkur’ani ba, kuma al’umma su gyara dabi’unsu domin Annabi alaihissalam ya ce ” An aikoni domin na gyara dabi’u”, kuma “La Dina liman La amanata Lahu”, duk wanda bashi da Amana bashi da Addini.
