Kasuwanci
Gwamnatin Tarayya Ta Tsawaita Wa’adin Lokacin Cire Tallafin Man Fetur
Gwamnatin tarayya na shirin tsawaita dakatarwar da ta yi na cire tallafin man fetur da watanni 18.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Mista Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Sylva ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen tunkarar majalisar dokokin kasar domin yin gyara ga dokar masana’antar man fetur (PIA).
